Dattawan PDP na taron dinke baraka

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan da Cif Olusegun Obasanjo

Dattawan jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya sun soma wani taro a Abuja don lalubo hanyoyin dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar, inda tuni wasu suka balle.

Datawan karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo no kokarin tattaunawa da duka bangarorin da basa jituwa da juna, musamman bangaren gwamononi bakwai da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wadanda ke ikirarin kafa 'sabuwar' PDP.

Kawo yanzu dai tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Ahmadu Ali na cikin dattawan dake kokarin sulhunta 'yan PDP din.

Wakilin BBC wanda ke babban otal na Abuja wato Trancorp Hilton inda ake taron, Abdou Halilou ya ce gwamnonin PDP da kuma na 'sabuwar' PDP irinsu Aliyu Wammako na jihar Sokoto da Rotimi Ameachi na jihar Ribas duk suna cikin wadanda ake ganawa dasu.

Tuni dai 'yan majalisar dattijai 22 dana wakilai 57 suka yi wa shugabannin 'sabuwar' PDP mubaya'a.

Karin bayani