Muna kan bakanmu a kan Syria —Putin

Image caption China da Rasha na goyon bayan Shugaba Assad

Amurka da Rasha ba su warware bambancin da ke tsakaninsu ba a kan batun amfani da matakin soji a kan Syria, kamar yadda Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana.

Mista Putin ya ce ba daidai ba ne a gudanar da wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Ya bayyana haka ne a taron manena labarai a rana ta karshe na taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a St Petersburg.

Shugaban Amurka, Barack Obama ya neman goyon bayan shugabannin kungiyar G20 a kan yinkurin kasarsa na yi wa Syria luguden wuta.

Amurka na zargin Shugaba Bashar al-Assad da kashe mutane 1,429 da makami mai guba a Damascus a ranar 21 ga watan Agusta.

Karin bayani