Twitter ya dakatar da shafin Alshabab

Image caption Karo na biyu kenan ana dakatar da shafin Alshbab

Dandalin sada zumunta na Twitter ya dakatar da shafin kungiyar masu fafutukar Islama ta Alshabab a karo na biyu.

A watan Janairu ne dai aka fara dakatar da shafin kungiyar, bayan ta yi barazanar kashe wasu 'yan kasar Kenya da take garkuw da su.

Kungiyar wacce ta sauya sunan shafinta bayan dakatarwan na farko, ta ce matakin Twitter na baya-bayan nan wani yunkuri ne mara tasiri na rufe gaskiya a game da Somalia.

Har yanzu dai bayanan kungiyar na larabci na cigaba da aiki.

Twitter na da dokar dakatar da duk wani mai amfani da dandalin da ya yi barazanar kai hari ko yin wasu ayyukan da suka saba doka.