Mun samu sabuwar shaida kan Syria - Cameron

Image caption Burtaniya za ta shiga gaba a tattaunawar da za a yi kan ayyukan jinkai a Syria a wajen taron.

Burtaniya ta ce ta samu sabuwar shaidar da ke nuna cewar gwamnatin Syria ta yi amfani da gubar Sarin kan fararen hulla.

Farayin Minista David Cameron ya shaidawa wakilin BBC a Rasha inda ya je domin halartar taron kungiyar G20 cewa masana kimiyya a Porton Down na ci gaba da bincike kan wasu ababe da aka debo daga babban birnin Syria.

Ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar da cewar sun samu alamun gubar Sarin a kan tufafi da kuma kasar da aka debo daga wajen da aka kai harin.

Sai dai ya ce kasarsa za ta shiga gaba wajen kiran kara samarwa 'yan gudun hijira tallafi kuma ta matsa kaimi wajen soma sabuwar tattaunawar zaman lafiya.

Karin bayani