An ceto daruruwan 'yan gudun hijira a teku

'Yan ci rani
Image caption 'Yan ci rani

Masu gadin gabar ruwayen Italiya sun ce, a kwanaki biyun da suka wuce sun ceto mutane fiye da dari bakwai daga jiragen ruwan da ke dauke da 'yan ci-rani da kuma 'yan gudun hijira.

Kananan jiragen ruwa cike makil da mutane daga Syria, da Masar, da Najeriya, da Ghana da kuma Eritrea, sun sami kansu cikin matsala a gabar tekun Sicily.

Dole sai da aka ruga da wasu mutane hudu, 'yan gida guda asibiti, saboda suna cikin mawuyacin hali.

A 'yan watannin nan an sami karuwar 'yan gudun hijirar da ke kokarin danganawa da Italiya, saboda tashin hankalin da ke kara ruruwa a Syria da Masar.