An kama barawo a fadar Buckingham

Fadar sarauniyar Ingila da ke Buckingham
Image caption Ana zargin mutumin da laifin sata da yin kutse da kuma barnata kayayyaki.

'Yan sanda a Burtani sun kama wani mutum da ake zargi da sata da yin kutse da kuma barnata kayayyaki, bayan ya tsallaka katangar fadar sarauniyar Ingila da ke Buckingham.

An dai kama shi ne a ranar litinin, a wani wuri da ake bari a bude dan mutane su shiga.

A bangare daya kuma an kama wani mutum na daban a wajen gidan Sarauniyar, da ake zargisa da kokarin yin kutse.

An dai bayyana cewa duka mutane biyun an bada belinsu, sai dai ana ci gaba da yin bincike akansu.

Haka nan iyalan masarautar ba sa nan a lokacin da abin ya faru.

Karin bayani