Nadin sabbin gwamnoni a Jamhuriyar Nijar

Shugaban kasar Nijar Mohamadou Issoufou
Image caption Shugaban kasar Nijar Mohamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar shugaban kasar Alhaji Mahamadu Isufu ya sa hannu a kan wani kudurin nada sabbin gwamnonin jahohin takwas a kasar.

Sabbin gwamnonin jahohin dai sun hada da 'ya'yan jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki da kuma wasu jam'iyu na kawancen MRN irin su ANDP Zaman Lafiya,da UDR Tabbas ,da wani na jam'iyar Moden Lumana duk da cewa jam'iyarsa ta fita daga kawancen da ke mulki.

Dangane da wannan garanbawul da shugaban kasar ya yi wa gwamnonin jihar takwas, biyu ne kadai tsofaffi, da suka hada da Alhaji AHmadu Babale na jam'iyar Moden Lumana, wanda a da yake rike da mukamin gwamnan jihar Bosso, a yaunzu an nada shi gwamnan jihar Maradi.

Daga cikin sabbin gwamnonin akwai Jabir Hasumi wani dan majalisar dokokin na jami'yar PNDS Tarayya.

Nade-nade dai ya biyo bayan garanbawul din da shugaban kasar ya yi, bayan da jam'iyar Moden Lumana ta dau matakin ficewa daga kawancen dake mulkin na MNR.