Boko Haram sun kashe mutane 15 a kasuwa

Boko Haram Najeriya
Image caption Boko Haram Najeriya

A jihar Borno, arewacin Najeriya wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka mutane 15 a wata kasuwa a yankin arewacin jihar.

'Yan bindigar sun abka cikin kasuwar kauyen Gajiram dake da tazarar kilomita 85 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, kana suka bude wuta.

Wasu mutanen kauyen sun shaidawa kamfanin dillacin labarai na 'Associated Press' cewa, maharan da suka yi bad da kama , sun shiga cikin garin a motocin a kori kura ne, kana suka shiga kasuwar suka bude wuta.

Galibin Hare-haren na faruwa yankunan karkara na jihar Bornon da ake dangantawa da daukar fansa.

Ya biyo bayan da kungiyar sa kan nan ta matasan jihar da aka fi sani da Civilian JTF suka fara gudanar aikin tallafawa hukumkomin tsaron wajen farautar 'yayan kungiyar ta Boko Haram.

Ko a cikin makon da ya gabata sai da wasau 'yan bindigar suka hallaka matasan akalla 24 , yayinda wasu karin 36 suka yi batan dabo, a garin Monguno dake arewacin jihar.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe masu tada kayar baya na kungiyar Boko Haram da ke arewa maso gabashin kasar hamsin.

Mai magana da yawun rundunar ya ce, dakarun su da ke jihar Borno sun je farautar 'ya'yan kungiyar ta boko haram a sansanonin su, inda anan ne suka kashe mutanen a wata musayar wuta da suka yi.

A watan Mayu ne shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a wasu jihohi uku da ke arewa maso gabashin Najeriya ciki har da jihar Borno.