Najeriya:An kasa samun matsaya a taron jam'iyar PDP

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Image caption Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

An kasa samun matsaya a taron da kwamitin amintattu na jam'iyar PDP a Najeriya, don dinke barakar da ta kunno kai a cikin jam'iyar.

Bangarorin biyu sun gana ne a lokuta daban-daban da mambobin kwamitin amintattu na jam'iyar.

Tsohon shugaban Najeriya olusegun Obasanjo ne ya jagoranci zaman da suka shafe kusan sa'o'i bakwai suna ganawa.

Chief Obasanjo ya shaidawa manema labari cewa, babu wani ci gaba na abin ku zo ku gani da aka samu a tattaunawar ta su.

Ya ce akwai sabani a cikin PDP da ake kokarin shawo kai kafin ya baci,amma an gana da duka bangarorin, kuma mataki na gaba shine a nemi sasantawa da juna.

A makon jiya ne dai, jam'iyyar ta dare gida biyu bayan da wasu gwamnoni da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar su ka fice daga cikin babban taron jam'iyyar da aka gudanar a Abuja, kana suka kafa abinda suka kira sabuwar PDP.