PDP: An rufe ofishin ɓangaren da ya ɓalle

Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami'an tsaro a Abuja sun rufe sakatariyar bangaren jam'iyyar PDP da ya balle a karkashin shugabancin Abubakar Kawu Baraje.

Hakan ya faru a daidai lokacin da ake kara samun baraka tsakanin bangaren Bamanga Tukur da wancan bangaren da ya kira kansa Sabuwar PDP.

Tuni dai bangaren Bamanga Tukur ya fitar da sanarwa yana yabawa matakin da 'yan sanda suka ɗauka na rufe ofishin bangaren PDP da ya ɓalle.

Koda jiya ma anyi wani taro na dattawa, amma aka kasa sasanta bangarorin na PDP dake takaddama.