Boko Haram: An kashe mutane 18 a Benisheik

'Yan kungiyar Matasan sa kai na jihar Borno
Image caption 'Yan kungiyar Matasan sa kai na jihar Borno

A jihar Borno arewacin Najeriya mutane 18 ne suka mutu, yayin arangama tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da kungiyar mayakan sa kai.

Lamarin ya faru ne a garin Beinisheik mai tazarar kilomita 72 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, kana kilomita 30 daga Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Rahotanni sun ce biyar daga cikin wadanda suka mutun 'yan kungiyar ta Boko Haram ne.

Wannna na zuwa ne mako guda bayan da wasu 'yan bindigar suka hallaka 'yan kungiyar matasa masu aikin samar da tsaro a jihar Borno 24, a garin Monguno dake arewacin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito cewa, kakakin rundunar hadin guiwar samar da tsaro a jihar Borno JTF Lt Col Sagir Musa ya tabbatar da abkuwar lamarin.

Ya ce yanzu haka dakarunsu na ci gaba da bincike a yankin, don farauto 'yan bindigar da suka arce.

Yayin da dai hakan ke faruwa, 'yan kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kaiwa matasan hari a yankuna daban-daban na jihar Bornon.

Sai dai kuma bayanai sun ce suma matasan na cewa duk da kalubale da barazanar da suke fuskanta, babu gudu ba ja daya baya wajen gudanar da aikin nasu.