An kashe mutane 18 a Beni Sheik

Image caption Matasa masu sa kai suna tallafawa rundunar JTF

Rahotanni daga Najeriya sun ce, mutane goma sha takwas sun rasa rayukansu, a artabun da aka yi tsakanin wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne, da kuma wasu 'yan banga a garin Beni Sheik dake jihar Borno.

An ce biyar daga cikin wadanda suka mutun, a fadan 'yan Boko Haram ne, yayin da sauran sha ukkun, 'yan banga ne.

Wannan tashin hankalin ya faru ne mako guda bayan da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka hallaka wasu 'yan banga fiye da ashirin a jahar ta Borno.

Masu aiko da rahotanni daga Najeriya na cewar, rundunar sojan kasar na karfafa wa jama'a gwiwar shiga banga, domin farautar 'yan Boko Haram din, yayin da sojojin su ma suke cigaba da kai masu hari.