An sace shugaban coci a Najeriya

Hoton gicciyen Yesu Kristi
Image caption Hoton gicciyen Yesu Kristi

A Najeriya ana cigaba da rokon Allah ya taimaka a sako wani shugaban cocin Anglican wanda wasu 'yan bindiga suka sace a ranar Juma'a.

Cocin ta Anglican ta ce an yi awon gaba da Reverend Ignatius Kattey, wanda shine na biyu a girman mukami a cocin, daga kusa da gidansa da ke birnin Patakwal.

An sace shi ne tare da matarsa Beatrice, to amma tuni aka sako ta.

Wakilin BBC a Lagos ya ce, ba a san dalilin da ya sa aka sace shugaban cocin ba, kuma kawo yanzu ba kungiyar da ta fito fili ta ce ita ta sace shi.