Syria: 'Yan tawaye sun kwace Maaloula

'Yan tawayen kasar Syria
Image caption 'Yan tawayen kasar Syria

Wasu 'yan tawayen kungiyar Nusra da ke da alaka da Al-Qaeda sun kwace kauyen Maaloula na Syria dake da nisan kilomita 55 daga arewacin Damascus.

'Yan tawayen Syria sun ce dakarun gwamnati sun janye, sai dai kuma kafofin yada labarai na gwamnatin sun ce ana cigaba da gwabza fada.

Akwai fargabar yiwuwar lalata kayayyakin tarihin kiristocin kauyen, inda har yanzu ke amfani da dadadden harshen Arminiyanci, yayinda aka bayar da rahoton kaiwa majami'u hari.

'Yan adawar Syria sun yi gargadin cewa, dakarun gwamnati sun yi ruwan bama-bamai akan wata babbar madatsar ruwa da ke tafkin Assad a arewacin kasar, abinda ke nuna barazanar abkuwar ambaliyar ruwa a yankin Euphrates.