Zadari ya sauka daga mulki

asif ali zadari
Image caption An yi ta sukan lamirin Zadari saboda almundahana

Asif Ali Zadari ya sauka daga mukamin shugabancin kasar Pakistan a karshen wa'adinsa na shekara biyar.

Shi ne shugaban farko da aka zaba na dumokradiyya da ya kammala cikakken wa'adinsa gaba daya.

Mr Zadari ya kama mulki ne bayan an kashe matarsa tsohuwar frai ministar kasar Benazir Bhutto a 2007.

A lokacin mulkinsa an yaba masa saboda tsattsauran matakin da ya dauka a kan masu gwagwarmayar musulmi.

A ranar Litinin za a rantsar da magajinsa Mamnoon Hussain.