CAR: An kashe mutane 60 a sabon rikici

Image caption Tsaffin 'yan tawaye na Seleka

Mutane akalla sittin sun mutu a tashin hankalin da aka yi tsakanin tsaffin 'yan tawaye da dakaru masu biyayya ga tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya wanda aka hambarar a watan Maris.

Kakakin shugaban kasar ya ce mayaka masu goyon bayan Francois Bozize sun kai hari a wani kauye dake arewa maso yammacin babban birnin.

Wannan ne hari mafi muni da magoya bayan tsohon shugaban sun kai un bayan da aka kifar dashi a wata Maris.

Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na da albarkatun kasa kamar zinare da lu'u-lu'u, amma tun bayan samun 'yancin kanta ba bu zaman lafiya.

A farkon wannan watan ne aka rantsar da Michel Djotodia, wato tsohon jagoran 'yan tawaye na Seleka a matsayin shugaban kasa.

Karin bayani