Nissan ya kirkiro agogon direbobi

Image caption Wani direba sanye da agogo

Kamfanin kera motoci na Nissan ya kaddamar da wani agogo komai da ruwanka, mai suna Nismo ga direbobin mota.

Nismo na kula da yadda mota ke aiki da yadda direba ke tuka ta, kana kamar saura agogo irinsa, yana auna bugun zuciya da yanayi da sauran bayanan halittar dan adam.

Haka kuma yana baiwa mai shi damar sanin yadda mota ke gudu da kuma man da take sha.

An kaddamar da agogon ne, gabannin bajekolin motoci na Frankfurt.

Image caption Samsung ne ya soma fitar da irin agogon

'Ra'ayin masana'

Masana sun ce agogon yana da muhimmanci, a yunkurin da zai kai ga samun hanyar sadarwa ta intanet a cikin mota.

Muhimmin abu dai shi ne kirkiro wata fasaha ga direbobin mota, wacce za ta iya gano gajiya da kuma yadda direba ke maida hankali a kan tuki da sauransu.

Nismo na zuwa ne cikin launuka uku, kuma batur din agogon na shafe tsawon mako guda, kana yana da gurin latsawa biyu a fuskarsa.

A baya-bayan nan an fito da agoguna samfurin komai da ruwanka da dama a kasuwa, wadanda suka hada da Galaxy Gear na Samsung da kuma na Sony.