'Yan sanda mata a Afghanistan

Wasu mata 'yan sanda a Afghanistan
Image caption Tsohon shugaban 'yan sanda a Kabul, Janar Ayub Salangi ya musanta zargin cin zarafin mata a rundunar

An haramta wa mata shiga aikin 'yan sanda a karkashin mulkin 'yan Taliban, amma bayan fiye da shekaru goma, gwamnatin Afghanistan ta kasa kara yawan 'yan sanda mata.

Wani rahoton kungiyar agaji ta Birtaniya Oxfam ya ce, yunkurin daukar mata 5,000 aikin 'yan sanda nan da karshen badi, abu ne dake da kamar wuya.

A yanzu 'yan sanda mata kasa da 1,600 ne a rundunar 'yan sandan Afghanistan, kuma akwai wasu kusan 200 dake yin horo, kuma har yanzu mata ba su fi kashi daya cikin dari na 'yan sandan kasar ba.

Birtaniya ce ke biyan kusan fam miliyan takwas na alabashin 'yan sanda, kuma tana son ganin 'yan sanda mata sun karu a kan titunan kasar, domin tabbatar da doka da oda.

Matsaloli

Cikin abubuwan dake janyo koma baya a daukar mata 'yan sanda, sun hada da al'adu da jahilci tsakanin mafi yawan mata da kuma tsoron cin zarafi.

BBC ta zanta da wata yarinya da wani dan sanda ya yiwa fyade, bayan ta gudu daga gidansu, amma daga bisani an daure shi.

Haka kuma akwai hujjojin dake nuna cewa, ana samun ayyukan cin zarafi a tsakanin 'yan sandan.

Rahoton na Oxfam ya ce a yawancin lokuta, mata 'yan sanda basu da kayan sarki kuma ba su da gurin canja kaya, ba su da inda za su kebe, kuma wasu shugabannin 'yan sanda basa karbar matan da aka dauka.

Parigul Saraj na aiki a wajajen binciken ababen hawa, wajen dake da hadari ga 'yan sanda saboda barazanar kai harin kunar bakin wake.

Aikinta shi ne binciken motoci da mata, saboda haramun ne ga namiji ya caje mata.

Ta ce gidansu da makota sun sallama ta, musamman saboda wasu lokuta a tan je aiki cikin dare, abin da ke tattare da tsangwama.