Algeria ta bai wa Nijar gudunmawar abinci

Mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Yamai a bara
Image caption Kimanin mutane dubu 70 ne ambaliyar ruwar ta rutsa da su a Nijar

Kasar Algeria ta taimaka wa jamhuriyar Nijar da wasu kayayyakin abinci, domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su.

A ranar Litinin ne jirgi na farko ya sauke kayayyakin a yamai, yayin da jirgi na biyu ake sa ran zai isa Nijar din a ranar alhamis mai zuwa.

Tallafin na Algeria ya biyo bayan kiran da gwamnatin Nijar ta yi wa abokan arzikinta, na su taimaka mata domin tunkarar matsalar ambaliyar da yankuna da dama na kasar ke fuskanta.

Algeria ta kuma mika wasu kayayyakin abincin ga kasar Mali, domin taimakwa wadanda ambaliyar ruwa ya rutsa da su.