An samu rabuwar kai game da Syria

Kwamitin  sulhun majalisar dinkin duniya
Image caption Kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya

An samu barakar Diplomasiya a Majalaisar dinkin duniya game da yadda za a aiwatar da shawarar da Rasha ta gabatar na saka makamai masu gubar Syria a karkashin kulawar kasashen duniya.

An soke wani taron kwamitin sulhun majalisar dinkin duniyar da aka shiryi yi bisa bukatar Rasha a kurarren lokaci.Amurka da Faransa da Birtaniya na shirya wani kuduri dake bayar da izinin yin amfani da karfi a kan Syria idan ta kasa kiyaye wa da bukatun ta mika tarin makamai masu gubarta a lalata.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha yayi watsi da duk wani shiri dake yin barazanar amfani da karfi.