Za a fara sauraron karar William Ruto a Hague

Willam Ruto lokacin yana shirin shiga Kotun ICC
Image caption Willam Ruto lokacin yana shirin shiga Kotun ICC

Yau ne za a fara sauraron shari'ar mataimakin shugaban kasar kenya William Ruto a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC.

Ana zargin Mr Ruto ne da kuma Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da laifin kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2007.

Alkalai a kotun sun ce za'a saurari kararrakin biyu ne a lokuta daban daban inda za'a samu ratar makwanni hudu a tsakaninsu.

Kusan shekaru shidda kenan bayan da kasar Kenya ta fada cikin tashe-tashen hankula sakamakon zaben da aka gudanar a shekara ta 2007 mai cike da takaddama, mataimakin shugaban kasar.

Rikicin da ya biyo bayan zaben dai ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu daya, kana dubu dari shida suka rasa matsugunai.