'Zan iya dakatar da matakin soji kan Syria'

Image caption Shugaba Obama

Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce zai iya dakatar da shirinsa na kaddamar da matakin soji a kan Syria idan har Syriar ta amince ta mika tarin makamanta masu guba karkashin kulawar kasa da kasa.

Amma ya ce da kamar wuya gwamnatin Syria tayi hakan.

A yayinda Majalisar dokokin Amurka ke mahawara a kan harin, Rasha a ranar Litinin ta bukaci Syria ta dakatar da batun makami mai guba.

Amurka na zargin Damascus da aikata laifukan yaki hadda amfani da makami mai guba, amma gwamnatin Syria ta musanta.

Shugaban Amurka ya yi hira da kafafen yada labarai daban-daban don neman goyon bayan al'ummar kasar da kuma 'yan majalisa a kan batun amfani da matakin soji a gabas ta tsakiya.

A cewar shugaban, ana bukatar amfani da takaitaccen matakin soji don hukunta Shugaba Bashar al-Assad saboda kada ya sake amfani da makami mai guba a nan gaba.

Karin bayani