Rasha ta nemi Syria ta mika makamanta

Makaman kasashen Rasha da Syria
Image caption Makaman kasashen Rasha da Syria

Rasha ta bukaci kasar Syria ta mika makamanta masu guba a lalata su, domin kauce wa matakin soji da Amurka ke barazanar dauka.

Rasha ta yi wannan tayin ne a wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajenta, Sargei Lavrov da takwaransa na Syria, Walid Muallem.

Shugaba Obama ya ce shawarar da Rasha ta yanke cewa Syria ta mika iko zai iya zama wani gagarumin cigaba.

Sai dai kuma a wasu jerin ganawar da ya yi da gidan talabjin, Mr Obaman na ci gaba da shakku, kana sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry zai ja hankalin Rashar kan yadda girman batun yake.

A lokaci guda kuma an dage batun kada kuri'ar da 'yan majalisar dattawa zasu kada akan yiwuwar daukar matakin soji kan kasar Syria.

Mr Obaman kuma ya hakikance cewa bashi da tabbacin zai samu goyon bayan 'yan majalisar dokokin, a duk wata kuri'a da za a kada game da shirin daukar matakin soji kan Syria.