Harin bam a shalkwatar sirrin Masar

Sojoji na rangadi a yankin Sinai cikin mota mai sulke
Image caption Wani dan kunar bakin wake ne dai tuka motar, inda ya kusa cikin ginin sojojin

An kai harin bam da wata mota a kan shalkwatar hukumar tattara bayanan sirri ta Masar, kuma mutane hudu sun mutu, a cewar gidan talabijin na kasar.

Haka kuma wasu mutane goma sun jikkata a harin na shalkwatar dake Rafah, a bakin iyakar Masar da Zirin Gaza.

Harin ya zo ne bayan kisan wasu masu fafutukar Islama tara, a wata arangama tsakaninsu da sojoji a yankin Sinai.

An kai wani harin kuma a wajen da sojoji ke binciken ababen hawa, a cewar kamfanin dillacin labarai na AFP, sai dai ba a tantance ko an samu rauni a harin ba.