Jonathan ya sallami ministoci tara

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Rahotanni a Najeriya sun ce Shugaba Goodluck Jonathan ya sauke wasu daga cikin ministocinsa.

An sauke ministocinne a lokacin taron mako mako na majalisar zartarwa da shugaba Jonathan ke jagoranta.

A garambawul din dai Shugaban na Najeriya ya sallami tara daga cikin ministocin nasa.

Korar ministocin ta bazata tazo ne a daidai lokacin da Jam'iyyar PDP mai jan ragamar mulkin kasar ke fama da matsala bayan da wasu gwamnoni bakwai suka balle karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar inda suka ce sun kafa 'Sabuwar PDP''.

Ministocin sune:Ruqayat Rufai (Ilimi); Zainab Kunchi (Makamashi); Bukar Tijani (Aikin gona), Shamsudeen Usman (Tsare-tsaren kasa) da Olusola Obada (Tsaro).

Sauran sune: Ita Okon (Kimiya da Fasaha); Olugbenga Ashiru (Harkokin kasashen waje); Ama Pepple (Kasa da sifiyo) da kuma Hadiza Mailafia (Muhalli).

Karin bayani