Kenya ta gano gulbi cike da ruwa

Image caption Yankin da aka gano gulbin na fama da matukar fari a Kenya

Gwamnatin Kenya ta bada sanarwar gano wani gulbin karkashin kasa da zai iya magance matsalar karancin ruwa a kasar na shekaru aru aru masu zuwa, lamarin da zai kyautata yanayin rayuwar al'ummar kasar.

Wannan gulbi na karkashin kasa dake yankin Turkana a arewa maso yammacin kasar ta Kenya, wasu masana kimiyya na suka gano shi ta hanyar amfani da na'urar binciken kimiyya mai aiki da tauraron dan adam.

Wasu koramu na karkashin kasa ne ke ba gulbin ruwa daga wasu tsaunuka masu nisa, kuma idan aka alkinta shi, ana jin da wuya ya taba kafewa.

Miliyoyin jama'a ne a kasar Kenya ba sa samun tsabtataccen ruwa.

Kasar na fama da kamfar ruwa, kuma sauyin yanayi zai iya tasiri a kanta.