An haramtawa limamai 18 wa'azi a Saudiyya

Image caption Sarki Abdallah na Saudiyya

Rahotanni daga Saudi Arabiya na nuna cewar an haramtawa malaman addini su 18 gabatar da hudubar Sallar Juma'a saboda bayanai na siyasa da suke yi.

Jaridar Al Hayat ta ambato wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin Islama na cewar malaman sun yi abubuwan da basu dace ba a lokacin hudubarsu, kuma ana musu tambayoyi.

Galibin masu wa'azin da aka dakatar sun fito daga lardin gabashin Saudiya inda ake samun tsirarun 'yan shi'a masu zanga-zanga.

Karin bayani