Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 10

Image caption 'Yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan kungiyar Boko Haram su 10 a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.

Kakakin rundunar a Borno, Laftanar Kanar Sagir Musa ya ce an kashe 'yan Boko Haram din ne bayan wata bata kashi sannan kuma sojoji suka yi luguden wuta ta sama a kan sansanin 'yan kungiyar dake kauyen Mada.

A cewarsa, sun kuma kwace makamai da wasu babura masu kafa uku na 'yan Boko Haram din a rangamar ta ranar Talata.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce a cikin wattani shida da suka wuce, an kashe mutane fiye da 230 a tashin hankalin da keda nasaba da Boko Haram a Najeriya.

Tun a watan Mayu, shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar don murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Karin bayani