Liberty Radio ta kai gwamnatin Kaduna kotu

Image caption Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na jihar Kaduna.

Gidan rediyo mai zaman kansa a jihar Kaduna, Liberty Radio ya gurfanar da gwamnatin jihar Kaduna gaban kuliya don ta warware takaddamar dake tsakaninsu.

Gwamnatin jihar Kaduna ta zargi gidan rediyon Liberty da kin biyan haraji abinda kuma yasa ta sa kafar wando daya da tashar.

A yayinda gidan rediyon Liberty ke zargin gwamnati da yi mata bita da kulli saboda baiwa 'yan adawa damar caccakar gwamnatin.

Masu sharhi na kallon danbarwar a matsayin abu dake da nasaba da siyasa, saboda farin jinin gidan rediyon Liberty a tsakanin masu saurare a jihar inda kuma 'yan adawa kan soki lamarin gwamnati, abinda gwamnati bata so.

Kakakin gwamnatin jihar Kaduna dai ya ce matakinsu na neman bayanai game da haraji na kan ka'ida.