Sojin Mali sun fafata da 'yan tawaye

'yan tawayen abzinawa
Image caption a watan Yuli bangarorin biyu suka sanya hannu a yarjejeniyar dakatar da bude wuta

Sojin Mali sun yi dauki-ba-dadi da mayakan a ware na abzinawa, a fada na farko da aka gwabza tun bayan da bangarorin biyu suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.

Rikicin da ya hada da kungiyar NMLA wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku ya auku ne a kusa da iyakar kasar Mauritania.

Kowane bangare dai na zargin dayan da tada rikicin, wanda wani sojan Mali ya yi gargadin cewa zai iya gurgunta yarjejeniyar zaman lafiyar.

Tashin hankalin ya faru ne mako daya bayan rantsar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar shugaban zai fara tattaunawar zaman lafiya da 'yan tawayen cikin kwanaki 60.