An hana gwamna Rotimi Amaechi shiga gida

A Najeriya, 'yan sanda a Patakwal, babban birnin jihar Rivers sun killace hanyar shiga gidan gwamnatin jihar kana suka hana gwamna, Rotimi Amaechi shiga gidan gwamnatin.

Gwamna Rotimi Amaechi ya ce ya dawo gida daga duba ayyuka tare da tsaffin abokan aikinsa Shugabannin majalisun jihohi ne.

Gwamnan dai ya je duba wasu ayyukan hanyoyi ne, amma da ya dawo gidan gwamnatin sai ya tarar da dumbin 'yan sanda sun kange hanyar shiga gidan gwamnatin.

Yanzu haka dai gwamnan yace, shi da 'yan tawagarsa sun rasa tayi.