Malaman Somalia sun yi fatawa kan Al-Shabab

Image caption Mayakan Al-Shabab

Malaman Musulunci su 160 a Somalia sun fitar da fatawa a kan kungiyar al-Shabab, inda suka ce kungiyar ba tada wuri a addinnin Musulunci.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan ne karon farko da malamai su ka yi fatawa a kan kungiyar wacce ke iko da galibin kauyukan Somalia.

A wani babban taro a birnin Mogadishu, malaman sun yi Allawadai da rikicin da al-Shabab ke tadawa a fadin kasar.

Sheikh Hassan Jaamai ya shaidawa BBC cewar sun yi taronne don a fayyace ko kungiyar nada hallaci a Islama, kuma fatawar da aka fitar itace kungiyar ba ta gwagwarmayar musulunci bane.

Karin bayani