Putin ya gargadi Amurka ta yi hattara

Shugaba Vladimir Putin na Rasha
Image caption Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gabatar da wani sako ga al'ummar amurka a kan Syria.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gabatar da wani sako ga al'ummar Amurka a kan Syria.

A wani sharhi da ya rubuta a jaridar New York Times, Putin ya yi gargadin cewa duk wani hari da Amurka za ta kai wa Syria, zai bude wani sabon babi ne na hare-haren ta'addanci, kuma zai iya gurgunta dokokin duniya.

Mr. Putin ya kuma soki Amurka da cewa mutane da dama fa a duniya, ba sa kallonta a matsayin abar koyi a tsarin dumokradiyya, illa kasar da ta dogara da amfani da karfin tuwo.

An wallafa sharhin ne a yayin da manyan jami'an Amurka da na Rasha, ke shirin tattauna shawarar Rasha game da makamai masu guba na Syria.

Karin bayani