An kai hari ofishin jakadancin Amurka

harin ofishin jakadancin Amurka a Herat
Image caption Dakarun kawance sun ce babu wata matsalar tsaro a ofishin yanzu

Dakarun Amurka da tallafin jami'an tsaron Afghanistan, sun samu nasarar kawar da wani hari da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Amurka, da ke birnin Herat.

Harin da aka kai da asuba ya fara ne da tashin wani bam da aka dana a mota, wanda ya rushe wani bangare na kewayen ofishin.

Abin da ya bai wa maharan damar shiga ciki aka shiga musayar wuta da su na tsawon lokaci.

Taliban ta sanar cewa ita ce ke da alhakin kai harin, wanda 'yan sandan Afghanistan biyu da kuma wani jami'in tsaro suka mutu.

Yayin da fararen hula 17 kuma suka jikkata.