Shafin Twitter zai sayar da hannun jari

shafin sadarwa na twitter
Image caption Shafin ya ce yana da mabiya sama da miliyan 200 a duniya

Kamfanin shafin sadarwa ta Intanet na Twitter ya bayyana cewa yana shirin sayar da hannun jarinsa ga jama'a.

Kamfanin ya ce ya mikawa hukumomin Amurka bayanan shirin sayar da hannun jarin.

Masu lura da al'amura sun yi kiyasin cewa darajar kamfanin na twitter za ta kai dala miliyan dubu goma.

Shirin sayar da hannun jarin nasa abu ne da aka dade ana tsammani.

Kasancewar kamfanin na daya daga cikin shafukan sada zumunta da sadarwa na intanet fitattu.

Tun bayan da shafin Facebook ya sayar da nasa hannun jarin a bara.