An yanke wa maza 4 hukuncin kisa a India

Image caption Wadanda aka kama da laifi

Wata kotu a India ta yanke wa mutane hudu maza hukuncin kisa saboda yiwa wata budurwa fyade da kuma hallaka ta a birnin Delhi.

An samu Mukesh Singh, Vinay Sharma, Akshay Thakur da Pawan Gupta da laifi a duk tuhumar da ake musu.

Alkalin kotun, Yogesh Khanna ya ce shari'ar ta fada wani rukuni da ba za a iya wani hukunci mai sassauci ba.

Budurwar mai shekaru 23, an kai mata hari ne a wata motar Bus a watan Disamba sannan ta mutu bayan makwanni biyu.

Lamarin ya janyo zanga-zanga a fadin kasar India abinda yasa aka kafa sabuwar doka kan fyade.

Tunda farko, masu zanga-zanga a wajen kotun sun bukaci an rataye mazan hudu.

Karin bayani