Afghanistan: Kasa ta danne Mahakan ma'adinai 40

Mahakar ma'adinai ta Afghanistan
Image caption Wani bangaren mahakar Kwal dake Abkhorak ce ta rufta

Jami'an Afghanistan a lardin arewacin Samangan sun ce masu aikin ceto na kokarin ceto masu hakar ma'adinai su arba'in da suka makale karkashin kasa.

Mai magana da yawun gwamnan Lardin Mohammed Saddiq Azizi ya ce mutanen na aiki ne a mahakar Kwal dake Abkhorak a lokacin da wani bangaren mahakar ya rufta.

Daya daga cikin rahotannin da ake samu na cewa wasu sun mutu amma ba a tabbatar ba.

Aikin hakar ma'adinai dai wani bangare ne dake karkashin kulawar gwamnati a Afghanistan

Karin bayani