An kama dan fashi ta komputa a Argentina

An kama dan fashi ta komputer a Argentina
Image caption Wani matashi mai jagorantar masu satar bayanan aika kudade na jama'a ya shiga hannu a Argentina

'Yan sanda a Argentina sun kama wani matashi dan shekara 19 da ake zargi da jagorantar gungun wasu masu satar bayanai ta kwamfuta wadanda suke kutse a shafukan aika kudade na duniya da kuma na 'yan caca.

Matashin da jami'ai ke wa lakabi da kwararren mai kutse ana zargin yana samun akalla dala 50, 000 a kowane wata daga dakinsa a birnin Buenos Aires.

A ranar da za a kama shi hukumomi sun dauke wutar lantarki a gaba dayan unguwar da yake, domin hana shi share wasu muhimman bayanai a kwamfutarsa.

'yan sandan sun ce sun kai shekara daya suna kokarin gano matashin.