Ana ci gaba da aikin ceto a Colorado

Barack Obama
Image caption Mutane biyu sun mutu a jahar Colarado

An kai masu gadin Kasa na Amurka zuwa jahar Colorado domin samar da abinci da kuma ruwan sha ga mutanen dake jiran a cece su bayan mummunar ambaliyar ruwa.

Yayinda ake ci gaba da gagarumin aikin domin taimakawa mutanen da ambaliyar ta rutsa da su, dakarun kasa sun kwashi kayayyaki a manya manyan motoci zuwa garin Lyons inda ambaliyar ruwan ta shafa.

Jiragen helicopta na kwashe mutane daga cikin kauyen Jamestown mai tsaunuka.

An bayyana cewa mutane hudu sun mutu a jahar Colarodo kuma wani jami'i ya bayyana cewa ba a san inda wasu mutane sama da dari biyu suka shiga ba.

Karin bayani