Masar ta gargadi masu zanga zanga

Masar
Image caption An zargi masu goyan bayan Morsi na sace 'yan jarida

Gwamnatin Masar ta gargadi masu zanga zangar Islama dangane da sanya shingaye akan tituna ko kuma muzgunawa 'yan jarida, bayan zanga zangar da aka gudanar a birnin Alkahira a ranar juma'a.

A wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin din Kasar, mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida Janar Hani Abdellatif ya zargi magoya bayan hanbararren Shugaban Kasar Mohammed Morsi da aikata abinda ya kira laifukan kawo cikas akan tituna da sace 'yan jarida.

Gargadin na zuwa ne wata daya daidai bayan da dakarun Kasar suka fatattaki magoya bayan Mohammed Morsi daga sansanoni biyu da sukai zaman dirshan, lamarin da yai sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Karin bayani