Najeriya:Rukunin farko na mahajjata sun sauka a Saudia

Maniyyata aikin Hajji a Najeriya
Image caption Maniyyata aikin Hajji a Najeriya

Rukunin farko na maniyatta aikin hajjin bana daga Maiduguri a jhar Borno arewacin Najeriya sun sauka a kasar Saudi Arabia a daren jiya.

Maniyyatan su sama da dari biyar ne suka tashi daga Maiduguri jihar Borno zuwa kasa mai tsarki suka sauka a birnin Madina.

A jiya ne mataimakin shugaban kasar, Namadi Sambo, ya kaddamar da shirin aikin hajjin na bana.

Ana sa ran kimanin mahajjata dubu saba'in da shidda ne daga Najeriya za su yi aikin hajjin bana.