'Yansanda sun tarwatsa malamai a Mexico

Tarzomar malamai a Mexico
Image caption Birnin Mexico yana fama da zanga zanga a makwannin nan saboda tsarin gwamnati kan ilimi

'Yan sanda a birnin Mexico sun fatattaki dubban malaman makaranta masu yajin aiki daga birnin bayan da suka fasa sansanin malaman da ke zanga zanga.

An baza Masu zanga zangar da suka bijirewa umarnin da aka ba su na ficewa daga dandalin Zocalo inda suka taru da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi.

Wasu daga cikinsu sun maida wa 'yan sandan martani ta hanyar jifansu da bama baman fetur abinda ya kai ga arangama tsakaninsu.

Gwamnatin ta ce tana son killace filin ne domin bikin ranar samun 'yancin kasar.

Karin bayani