Tashin hankali tsakanin Eggon da Alagon

Rikici a Najeriya
Image caption Rikici a Najeriya

Rahotanni daga jihar Nasarawa dake arewa ta tsakiyar Nijeriya na cewa an samu hasarar rayukan mutane da dama da kuma kona dimbin gidaje a wani tashin hankali da aka yi a yankin Obi da kuma Asakyo.

'Yan-kabilar Alago ke zargin 'yan kabilar Eggon na kungiyar nan ta masu bin addini gargajiya da ake kira Ombatse da kai masu farmaki, inda suka kashe da dama daga ‘yan kabilar Alagon baya ga kona masu gidaje.

Har ila yau rahotanin sun ce yan kabilar Eggon din sun fatattaki 'yan-kabilar Alagon daga garuruwan da suke zaune, amma ‘yan kabilar ta Eggon na musanta zargin fara kai hari, suna cewa su ma a halin yanzu an kashe mutanensu kimanin talatin.

Tun a jiya ne dai tashin hankalin ya fara a kauyen Odobu dake karamar hukumar Obi, sannan da safiyar yau kuma sai tarzomar ta bazu zuwa cikin garin Obi inda rahotanni ke cewa akasarin mazauna garin yan kabilar Alago, sun gudu sakamakon farmakin na ‘yan kabilar Eggon.