An sako Archbishop Ignatius Kattey

Archbishop Ignatius Kattey
Image caption Archbishop Ignatius Kattey

An sako daya daga cikin manyan shugabannin cocin Anglican a Najeriya wanda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi fiye da mako guda kenan.

Wani jami'in 'yan sanda ya ce, da yammacin jiya ne aka sako Archbishop Ignatius Kattey, kuma lafiyarsa kalau.

An sace shi ne kusa da gidansa a birnin Patakwal a yankin Niger Delta, tare da uwargidansa.

Amma ita an sako ta tun tuni.

A wannan shiyyar Najeriya dai, satar jama'a don neman kudin fansa ta zama ruwan dare.

To amma a wannan karon, ba a san ko an biya wasu kudade ba, kafin sako shugaban cocin na Anglican.