Bikin Aure: Mutane 14 sun mutu a Kebbi

Image caption Alhaji Saidu Usman Dakingari Gwamnan jahar Kebbi

Rahotanni daga Najeriya sun ce mutane 14 cikin har da 7 'yan gida guda sun mutu a cikin wani kogi a jahar Kebbi dake arewa maso yammacin kasar.

Mutanen sun gamu da ajalinsu ne lokacin da wata karamar mota kirar Starlet da suke tafiya a ciki ta kauce hanya a kan wata gada ta fada cikin kogi da tsakiyar daren lahadi.

Hon. Samaila Mohammed Bagudo shugaban karamar hukumar Bagudo inda lamarin ya faru ya shaidawa BBC cewar wadanda lamarin ya rutsa dasu sun hada da mata 6 da maza 8; sai dai mutum daya ya tsira da ransa.

''Dukkansu mun yi jana'izarsu a nan makabartar garin Kende, mutum daya wanda kuma ke jinya kuma mun garzaya da shi zuwa asibitin Dakingari domin neman Magani.'' Inji shi.

Karin bayani