Neman goyan bayan diplomasiya kan Syria

Ali Haidar, ministan Syria
Image caption Ali Haidar, ministan Syria

Wani minista a gwamnatin Syria ya bayyana yarjajeniyar da aka cimmawa tsakanin Amirka da Rasha, don lalata makaman Syriar masu guba, a karkashin jagorancin majalisar dinkin duniya da cewa, nasara ce ga kasarsa.

A cewar ministan mai kula da sasantawa, Ali Haidar, yarjajeniyar ta taimaka wa Syria fita daga sarkakiya, da kuma kauce wa yaki.

Yayi kalaman nasa ne yayin da ake cigaba da kai-kawon diplomasiyya, na nema wa yarjajeniyar goyon baya.

Shi kuma ministan watsa labaran Syriar, Omran al-Zoubi, ya shaida wa gidan talabijin din ITV na nan Birtaniya cewa, kasarsa ta dauki yarjajeniyar da muhimmancin gaske, kuma tuni ta shiga shirya takardu na bayyanin makamanta masu guba.

An bata wa'adin mako guda na ta yi hakan.

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ce akwai yiwuwar nan da karshen mako, kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya kada kuri'a a kan yarjajeniyar.

Sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry, ya gana da Praministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu wanda ya ce suna fatan za a gani a kasa, bayan yarjajeniyar da aka yi tsakanin Amirka da Rasha, kan makamai masu gubar na Syriar.