An sanar da mutumin da yayi kisa a Amurka

An killace wajen da akai harbin
Image caption 'Yan sanda na ci gaba da binciken wadanda suka aikata harbin

Mutane 12 da suka hada da wanda ake zargin dan bindiga ne, sun rasa rayukansu a wani harbi da aka yi a wani ginin sojin ruwan Amurka dake tsakiyar birnin Washington.

An bayyana wanda ake zargi da cewar shi ne ya yi harbin, Aran Alaxes mai shekaru 34 a duniya, kuma ya taba aiki tare da sojin ruwan Amurkan a baya, har ya zuwa shekara ta 2011.

An dai rufe ofishin 'yan majalisar dattawan Amurkan da ke kusa da inda aka yi harbin, na wucin gadi.

Shugaba Obama ya jajanta abin da ya faru, sannan kuma ya tausayawa wadanda abin ya shafa.

Karin bayani