An kashe mutane 50 a Nassarawa

An kashe fiye da mutane hamsin a tashin hankalin kabilanci da aka yi a karshen mako a jihar Nassarawa dake Najeriya.

An gwabza fadan ne tsakanin 'yan kabilar Eggon masu rinjaye da kuma 'yan kabilar Alago wadanda tsiraru ne.

Rahotanni sun nuna cewar kawo yanzu an sama lafawar lamura a garin.

A watan Mayun da ya wuce ne, wasu 'yan kungiyar asiri na kabilar Eggon wadanda ake kira 'Ombatse' suka yi wa jami'an tsaron Najeriya kwantar bauna suka kashe akalla jami'an 65.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da jami'an tsaro suke kan hanyarsu ta damke shugaban kungiyar 'Ombatse', inda mabiyansa suka yi wannan kwantar baunan.