Masar: Jami'an tsaro sun karbe Dalga

Kristoci kibdawa a garin Dalga
Image caption Kristoci kibdawa a garin Dalga

A Masar 'yan sanda da soja da tallafin jiragen sama masu saukar ungulu sun aukawa wani gari dake karkashin ikon magoya bayan, Muhammad Morsi tsawon watanni biyu.

Wani jami'in tsaro yace, hukumomi sun kwace iko da garin Dalga, dake da nisan kilomita kusan dari uku daga babban birnin kasar.

Kauyen dai ya kasance ba a karkashin ikon gwamnati ba, tun daga farkon watan Yuli, yayin da masu kaifin kishin Islama dake goyon bayan Morsi suka fatattaki 'yan sandan garin.

Kristoci kibdawa sun yi korafin cewa, masu kaifin kishin Islaman suna karbar kudi daga hannunsu.