Zaki ya kashe mai kula da shi a kasar Habasha

Zaki a birnin Addis Ababa na kasar Habasha
Image caption Zaki a birnin Addis Ababa na kasar Habasha

Wani zaki ya hallaka mai kula da shi a gidan ajiyar namun daji da ke birnin Addis Ababa, babban birnin kasar habasha.

Zakin wanda aka lakabawa suna Kenenisa, sunan wani fitaccen magujin kasar ta Habasha, ya hallaka mutumin ne lokacin da yake share Kejin sa.

Rahotanni sun ce mutumin ya manta ya rufe kofar wurin da zakin ke barci ne, inda abokan aikinsa suka rika harbi ta sama don tsoratar da zakin.

Gidan ajiyar namun dajin na Addis Ababa, wanda sarki Haile Selassie na wancan lokacin ya bude a shekara 1948, na da zakokokin Abyssinia 15 masu hadarin gaske.